Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 17:23-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Amma duk da haka ba su kasa kunne, ko su mai da hankali ba. Amma suka taurare don kada su ji, su karɓi koyarwa.

24. “ ‘Amma idan kun kasa kunne gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofin wannan birni a ranar Asabar ba, amma kuka kiyaye ranar Asabar da tsarki, ba ku yi aiki a cikinta ba,

25. sa'an nan ne sarakuna waɗanda za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda, za su shiga ta ƙofofin wannan birni, suna hawan karusai, da dawakai, su da sarakunansu, da jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima. Za a zauna a wannan birni har abada.

26. Mutane za su zo daga biranen Yahuza da wuraren da yake kewaye da Urushalima, daga ƙasar Biliyaminu, da ta Shefela, da ta ƙasar tuddai, da kuma ta Negeb, suna kawo hadayu na ƙonawa da sadakoki, da hadayu na sha, da na turare, za su kuma kawo hadayu na godiya a Haikalin Ubangiji.

27. Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.’ ”

Karanta cikakken babi Irm 17