Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 13:17-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Amma idan ba za ku ji ba,Raina zai yi kuka a ɓoye sabodagirmankanku,Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za suzub da hawaye,Domin an kai garken Ubangiji zuwabauta.

18. Ubangiji ya ce wa Irmiya,“Ka faɗa wa sarki da sarauniya,uwarsa, su sauka daga gadonsarautarsu,Domin an tuɓe kyakkyawan rawaninsarautarsu daga kansu.

19. An kulle biranen Negeb,Ba wanda zai buɗe su,Yahuza duka an kai ta zaman dole,Dukanta an kai ta zaman dole.

20. “Ku ta da idanunku, ku ga waɗandasuke zuwa daga arewa!Ina kyakkyawan garken nan da akaba ku?

21. Me za ku ce sa'ad da aka naɗa mukushugabanni,Waɗanda ku da kanku kuka koyamusu, suka zama abokanku?Ashe, azabai ba za su auko muku baKamar yadda sukan auko wa macemai naƙuda?

22. Idan kun ce a zuciyarku,‘Me ya sa waɗannan abubuwa sukasame mu?’Saboda yawan zunubanku ne,Shi ya sa an tone tsiraicinku,Aka wahalshe ku.

23. Mutumin Habasha zai iya sākelaunin fatar jikinsa?Ko kuwa damisa za ta iya sākedabbare-dabbarenta?Idan haka ne, ku kuma za ku iya yinnagarta,Ku da kuka saba da yin mugunta.

24. Zan warwatsar da kuKamar yadda iskar hamada takewatsar da ƙaiƙayi.”

25. Ubangiji ya ce, “Wannan shi nerabonku,Rabon da na auna muku, ni Ubangijina faɗa.Domin kun manta da ni, kun dogaraga ƙarairayi,

26. Ni kaina kuma zan kware mukusuturarku ta rufe fuskarkuDon a ga tsiraicinku.

27. Na ga abubuwanku masubanƙyama,Wato zinace-zinacenku, da haniniyakamar dawakai,Da muguwar sha'awarku takaruwanci a kan tuddai da filaye,Ya Urushalima, taki ta ƙare!Har yaushe za a tsarkake ki?”

Karanta cikakken babi Irm 13