Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 12:8-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Abin gādona ya zama mini kamarzaki a cikin kurmi,Ya ta da murya gāba da ni,Domin haka na ƙi shi.

9. Ashe, abin gadon nan nawa ya zamadabbare-dabbaren tsuntsun nan nemai cin nama?Tsuntsaye masu cin nama sun kewayeshi?Tafi, ka tattaro namomin jeji,Ka kawo su su ci.

10. Makiyaya da yawa sun lalatar dagonar inabina.Sun tattake nawa rabo,Sun mai da nawa kyakkyawan rabokufai da hamada.

11. Sun maishe shi kufai, ba kowa,Yana makoki a gare ni,Ƙasar duka an maishe ta kufai,Amma ba wanda zuciyarsa ta damu akan wannan.

12. A kan dukan tsaunukan nan nahamadaMasu hallakarwa sun zo,Gama takobin Ubangiji yana ta kisaDaga wannan iyakar ƙasa zuwawaccan,Ba mahalukin da yake da salama.

13. Sun shuka alkama, sun girbeƙayayuwa,Sun gajiyar da kansu, amma ba suamfana da kome ba.Za su sha kunya saboda abin da sukegirbe,Saboda zafin fushin Ubangiji.”

14. Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra'ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama'arsa Isra'ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu.

Karanta cikakken babi Irm 12