Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 12:13-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sun shuka alkama, sun girbeƙayayuwa,Sun gajiyar da kansu, amma ba suamfana da kome ba.Za su sha kunya saboda abin da sukegirbe,Saboda zafin fushin Ubangiji.”

14. Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra'ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama'arsa Isra'ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu.

15. Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa.

16. Zai zama kuwa, idan za su himmantu su koyi al'amuran jama'ata, su yi rantsuwa da sunana, su ce, ‘Da zatin Ubangiji,’ kamar yadda suka koya wa jama'ata yin rantsuwa da Ba'al, sa'an nan za a gina su a tsakiyar jama'ata.

17. Amma idan wata al'umma za ta ƙi kasa kunne, to, sai in tumɓuke ta ɗungum, in hallaka ta, in ji Ubangiji.”

Karanta cikakken babi Irm 12