Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Hab 3:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Duwatsu sun gan ka, sun ƙame,Ruwaye masu hauka suka gudu.Zurfi kuma ya ta da muryarsa,Raƙuman ruwansa sun tashi.

11. Rana da wata sun tsaya cik a inda suke,A lokacin da kibanka masu haske suke wucewa fyu,Da lokacin walƙatawar hasken māshinka.

12. Ka ratsa duniya da hasala,Ka kuma tattake al'umman duniya da fushi.

13. Ka fito saboda ceton mutanenka,Saboda ceton shafaffenka kuma.Ka fasa kan mugu,Ka kware shi daga cinya zuwa wuya.

14. Ka kuje kan mayaƙansa da sandunansa,Waɗanda suka zo kamar guguwa don su watsar da mu.Suna murna kamar waɗanda suke zaluntar matalauci a ɓoye.

15. Ka tattake teku da dawakanka,Da haukan ruwa mai ƙarfi.

16. Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa,Leɓunana suka raurawa.Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki.Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zoA kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.

Karanta cikakken babi Hab 3