Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa,Leɓunana suka raurawa.Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki.Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zoA kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.