Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Hab 3:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Addu'ar nasara wadda annabi Habakuk ya yi.

2. Ya Ubangiji, na ji labarinka,Sai tsoro ya kama ni.Ka maimaita manyan ayyukanka a zamaninmu,Ayyukan da ka saba yi.Ka yi jinƙai ko lokacin da kake fushi.

3. Daga Edom Allah ya zo,Daga dutsen Faran Mai Tsarki yake tahowa.Ɗaukakarsa ta rufe sammai,Duniya kuwa ta cika da yabonsa.

4. Walƙiyarsa kamar hasken rana ce,Haske yana haskakawa daga gare shi,A nan ne ya lulluɓe ikonsa.

5. Annoba tana tafe a gabansa,Cuta kuma tana bin bayansa kurkusa.

6. Ya tsaya, ya auna duniya,Ya duba, sai ya girgiza al'umman duniya.Sa'an nan madawwaman duwatsu suka farfashe,Madawwaman tuddai kuma suka zama bai ɗaya.Haka hanyoyinsa suke tun adun adun.

7. Na ga alfarwan Kushan suna cikin azaba,Labulen ƙasar Madayana suna rawar jiki.

8. Ya Ubangiji, ka hasala da koguna ne?Ko kuwa ka yi fushi da koguna?Ko kuwa ka hasala da teku ne,Sa'ad da ka hau dawakanka, kana bisa karusarka ta nasara?

9. Ka ja bakanka,Ka rantsar da sandunan horo.Ka rarratsa duniya da koguna.

10. Duwatsu sun gan ka, sun ƙame,Ruwaye masu hauka suka gudu.Zurfi kuma ya ta da muryarsa,Raƙuman ruwansa sun tashi.

11. Rana da wata sun tsaya cik a inda suke,A lokacin da kibanka masu haske suke wucewa fyu,Da lokacin walƙatawar hasken māshinka.

12. Ka ratsa duniya da hasala,Ka kuma tattake al'umman duniya da fushi.

Karanta cikakken babi Hab 3