Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 9:5-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Gobe ne zan aikata al'amarin nan a ƙasar.”’

6. Kashegari kuwa Ubangiji ya aikata al'amarin. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, na Isra'ilawa kuwa, ko ɗaya bai mutu ba.

7. Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.

8. Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna, “Dibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa ta sama a gaban Fir'auna.

9. Tokar za ta zama kamar ƙura a dukan ƙasar Masar, ta zama marurai, suna kuwa fitowa a jikin mutum da dabba a dukan ƙasar Masar.”

10. Sa'an nan suka ɗauko toka daga matoya, suka tsaya a gaban Fir'auna. Da Musa ya watsa ta sama, sai ta zama marurai suna ta fitowa a jikin mutum da dabba.

11. Amma masu sihirin suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran, gama suka kamu da maruran kamar sauran Masarawa.

12. Ubangiji kuma ya taurare zuciyar Fir'auna har ya ƙi jin Musa da Haruna kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa wa Musa.

13. Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka je ka sami Fir'auna, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.

14. A wannan karo, ni da kaina zan kawo maka, da fādawanka, da jama'arka annoba, domin ka sani babu mai kama da ni a dukan duniya.

15. Gama da ni kaina na miƙa dantsena na buge ka da jama'arka da annoba, ai, da an hallakar da ku a duniya ƙaƙaf.

16. Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya.

17. Har yanzu kana fariya a kan jama'ata, ba ka sake su ba.

18. Gobe war haka zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske irin wadda Masar ba ta taɓa gani ba tun kafawarta, har zuwa yanzu.

19. Yanzu fa, sai ka ba da umarni a lura da awaki, da dukan abin da yake naku wanda yake a saura, gama duk mutum ko dabba wanda ya ragu a saura, wato wanda ba a kawo shi gida ba, zai mutu sa'ad da ƙanƙarar ta zo.”’

20. Akwai waɗansu daga cikin fādawan Fir'auna waɗanda suka tsorata saboda abin da Ubangiji ya faɗa, sai suka kawo bayinsu da dabbobinsu cikin gida.

Karanta cikakken babi Fit 9