Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 9:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je ka wurin Fir'auna, ka faɗa masa cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na Ibraniyawa, na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.

2. Amma idan ka ƙi sakinsu, wato kana ta riƙonsu,

3. to, hannuna zai auka wa dabbobinka cikin sauruka, da dawakai, da jakai, da raƙuma, da shanu, da tumaki, da awaki, da annoba mai tsanani.

4. Zan raba tsakanin dabbobin Isra'ilawa, da na Masarawa. Ko ɗaya daga cikin dabbobin Isra'ilawa ba zai mutu ba. Na riga na sa lokacin.

5. Gobe ne zan aikata al'amarin nan a ƙasar.”’

6. Kashegari kuwa Ubangiji ya aikata al'amarin. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, na Isra'ilawa kuwa, ko ɗaya bai mutu ba.

7. Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.

8. Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna, “Dibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa ta sama a gaban Fir'auna.

9. Tokar za ta zama kamar ƙura a dukan ƙasar Masar, ta zama marurai, suna kuwa fitowa a jikin mutum da dabba a dukan ƙasar Masar.”

10. Sa'an nan suka ɗauko toka daga matoya, suka tsaya a gaban Fir'auna. Da Musa ya watsa ta sama, sai ta zama marurai suna ta fitowa a jikin mutum da dabba.

11. Amma masu sihirin suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran, gama suka kamu da maruran kamar sauran Masarawa.

Karanta cikakken babi Fit 9