Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 4:17-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Za ka riƙe wannan sanda a hannunka, da shi za ka aikata mu'ujizan.”

18. Musa ya koma wurin Yetro, surukinsa, ya ce masa, “Ina roƙonka, ka bar ni in koma wurin 'yan'uwana a Masar, in ga ko a raye suke har yanzu.”Sai Yetro ya ce wa Musa, “Ka tafi lafiya.”

19. Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa a Madayana, ya koma Masar, gama dukan waɗanda suke neman ransa sun rasu.

20. Saboda haka Musa ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa maza, ya haushe su bisa kan jaki, ya koma ƙasar Masar, yana riƙe da sandan Allah a hannunsa.

21. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Sa'ad da ka koma Masar, sai ka kula, ka aikata a gaban Fir'auna dukan mu'ujizan da na sa cikin ikonka. Amma zan taurara zuciyarsa, don kada ya bar jama'a su fita.

22. Za ka ce wa Fir'auna, Ubangiji ya ce, ‘Isra'ila ɗan fārina ne.

23. Na ce maka ka bar ɗana ya tafi domin ya bauta mini, amma in ka ƙi ka bar shi ya tafi, yanzu zan kashe ɗan fārinka.”’

24. Ya zama kuwa sa'ad da Musa yake masauki a kan hanya sai Ubangiji ya gamu da shi, ya nema ya kashe shi.

25. Sai Ziffora ta ɗauki ƙanƙara ta yanke loɓar ɗanta, ta taɓa gaban Musa da shi, ta ce, “Kai angon jini kake a gare ni.”

26. Sa'an nan Ubangiji ya ƙyale shi. Ta kuma ce, “Kai angon jini ne,” saboda kaciyar.

27. Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi, ka taryi Musa cikin jeji.” Ya kuwa tafi ya tarar da shi a dutsen Allah, ya sumbace shi.

28. Sa'an nan Musa ya faɗa wa Haruna abubuwan da Ubangiji ya aike shi ya yi, da dukan mu'ujizan da ya umarce shi ya aikata.

29. Sai Musa da Haruna suka tafi suka tattara dukan dattawan Isra'ila.

30. Haruna dai ya hurta wa dattawan al'amuran da Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuma aikata mu'ujizan a idanunsu.

31. Dattawan kuwa suka gaskata. Sa'ad da suka ji Ubangiji ya ziyarci Isra'ilawa, ya kuma ga wahalarsu, sai suka sunkuya, suka yi masa sujada.

Karanta cikakken babi Fit 4