Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 35:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Kowane ne wanda ya iya, ya ba da sadaka ta azurfa, da ta tagulla ga Ubangiji. Duka kuma wanda aka iske shi yana da itacen ƙirya wanda zai yi amfani a cikin aikin, ya kawo shi.

25. Dukan mata masu hikima suka kaɗa zare da hannuwansu, suka kawo zaren da suka kaɗa na shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

26. Sai kuma dukan mata masu hikima, waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki.

27. Su shugabanni suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

28. Suka kuma kawo kayan yaji, da man fitila, da man keɓewa, da turaren ƙonawa.

29. Sai dukan mata da maza na Isra'ilawa waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kawo kowane irin abu domin yin aikin da Ubangiji ya umarci Musa. Suka kawo sadaka ta yardar rai ga Ubangiji.

30. Sai Musa ya ce wa Isra'ilawa, “Ga shi, Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuza.

31. Ya cika shi da ruhu na hikima, da basira, da sani, da fasaha na iya yin kowane irin aiki.

Karanta cikakken babi Fit 35