Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 35:22-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato da 'yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji.

23. Kowane mutum da aka iske shi yana da shuɗi, ko shunayya, ko mulufi, ko lallausan lilin, ko gashin awaki, ko fatun raguna da aka rina suka zama ja, ko fatun awaki, ya kawo su.

24. Kowane ne wanda ya iya, ya ba da sadaka ta azurfa, da ta tagulla ga Ubangiji. Duka kuma wanda aka iske shi yana da itacen ƙirya wanda zai yi amfani a cikin aikin, ya kawo shi.

25. Dukan mata masu hikima suka kaɗa zare da hannuwansu, suka kawo zaren da suka kaɗa na shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.

26. Sai kuma dukan mata masu hikima, waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kaɗa zare da gashin awaki.

27. Su shugabanni suka kawo duwatsu masu daraja da za a jera a kan falmaran da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

28. Suka kuma kawo kayan yaji, da man fitila, da man keɓewa, da turaren ƙonawa.

29. Sai dukan mata da maza na Isra'ilawa waɗanda zuciyarsu ta iza su, suka kawo kowane irin abu domin yin aikin da Ubangiji ya umarci Musa. Suka kawo sadaka ta yardar rai ga Ubangiji.

Karanta cikakken babi Fit 35