Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 34:21-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. “Cikin kwana shida za ku yi aiki, amma a kan rana ta bakwai sai ku huta, ko lokacin noma ne, ko lokacin girbi sai ku huta.

22. “Ku kuma kiyaye idin mako, wato idin girbin nunan fari na alkama, da idin gama tattara amfanin gonaki a ƙarshen shekara.

23. “Sau uku cikin shekara mazajenku duka za su hallara a gabana, ni Ubangiji Allah na Isra'ila.

24. Gama zan kori al'ummai daga gabanku, in fāɗaɗa kan iyakarku. Ba wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokatan nan uku na shekara da kukan hallara a gaban Ubangiji Allahnku.

25. “Ba za ku miƙa jinin hadayata tare da abinci mai yisti ba, kada kuma a bar hadaya ta Idin Ƙetarewa ta kwana.

26. “Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku.“Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.”

27. Ubangiji ya kuma ce wa Musa, “Rubuta waɗannan kalmomi, gama daidai suke da kalmomin alkawarin da suke tsakanina, da kai, da Isra'ila.”

28. Musa kuwa yana tare da Ubangiji yini arba'in da dare arba'in, bai ci ba, bai sha ba. Sai ya rubuta kalmomin alkawarin a kan allunan, wato dokokin nan goma.

29. Sa'ad da Musa ya sauko daga Dutsen Sina'i da alluna biyu na alkawarin a hannunsa, ashe, bai sani ba, amma fuskarsa tana annuri saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji.

30. Sa'ad da Haruna da dukan jama'ar Isra'ila suka ga fuskar Musa tana annuri, suka ji tsoro su kusace shi.

31. Sai Musa ya kirawo Haruna tare da shugabannin jama'ar duka, suka zo wurinsa, shi kuwa ya yi magana da su.

32. Daga nan jama'ar Isra'ila duka suka matsa kusa, Musa kuwa ya ba su dukan dokoki waɗanda Ubangiji ya ba shi a bisa Dutsen Sina'i.

Karanta cikakken babi Fit 34