Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 33:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi, ka kama hanya, kai da jama'ar da ka fisshe su daga ƙasar Masar, zuwa ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, na ce, ‘Ga zuriyarka zan ba da ita.’

2. Zan kuwa aiki mala'ika a gabanka. Zan kuma kori Kan'aniyawa da Amoriyawa, da Hittiyawa, da Farizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

3. Ka kama hanya zuwa ƙasa mai yalwar abinci, amma fa ba zan tafi tare da ku ba, gama ku mutane ne masu taurin kai, domin kada in hallaka ku a hanya.”

4. Da jama'ar suka ji wannan mugun labari, sai suka yi nadama. Ba wanda ya sa kayan ado.

5. Gama Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurin kai. In na yi tafiya tare da ku, nan da nan zan hallaka ku. Domin haka fa, yanzu, ku tuɓe kayan adonku, domin in san abin da zan yi da ku.”’

6. Domin haka Isra'ilawa suka tuɓe kayan adonsu tun daga dutsen Horeb har zuwa gaba.

7. Musa ya ɗauki alfarwa, ya kafa ta a bayan zango, nesa da zango. Ya kuwa sa mata suna, Alfarwa ta Sujada. Duk wanda yake neman Ubangiji, sai ya tafi alfarwa ta sujada, wanda yake a bayan zango.

8. Duk sa'ad da Musa ya tafi wurin alfarwar, jama'a duka sukan tashi tsaye, kowa ya tsaya a ƙofar alfarwarsa, ya kallaci Musa, har ya shiga alfarwar.

9. Sa'ad da Musa ya shiga alfarwar, al'amudin girgije ya sauko ya tsaya bisa ƙofar alfarwar, Ubangiji kuma ya yi magana da Musa.

10. A sa'ad da jama'a suka ga al'amudin girgijen nan na tsaye a ƙofar alfarwar, sai jama'ar duka su tashi su yi sujada, kowa a ƙofar alfarwarsa.

11. Ta haka Ubangiji ya riƙa yin magana da Musa baki da baki, kamar yadda mutum yakan yi magana da amininsa. Sa'ad da Musa ya koma cikin zango kuma, baransa, Joshuwa, ɗan Num, saurayi, ba zai fita daga cikin alfarwar ba.

12. Musa ya ce wa Ubangiji, “Ga shi, ka faɗa mini cewa, ‘Ka fito da mutanen nan,’ amma ba ka sanar da ni wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi kuma, ka ce, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a gare ni.’

13. Yanzu ina roƙonka idan na sami tagomashi a gare ka, ka nuna mini hanyoyinka domin in san ka, in kuma sami tagomashi a wurinka, ka kuma tuna, wannan al'umma jama'arka ce.”

Karanta cikakken babi Fit 33