Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 31:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

13. “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.

14. Ku kiyaye ranar Asabar gama tsattsarkar rana ce a gare ku. Duk wanda ya tozarta ta, za a kashe shi, duk wanda ya yi aiki kuma a cikinta za a raba shi da jama'arsa.

15. A kwana shida za a yi aiki, amma rana ta bakwai ranar hutawa ce tsattsarka ta saduda ga Ubangiji, don haka duk wanda ya yi kowane irin aiki a cikinta za a kashe shi.

16. Domin wannan fa Isra'ilawa za su kiyaye ranar Asabar, su kiyaye ta dukan zamanansu, gama madawwamin alkawari ne.

17. Ranar za ta zama dawwamammiyar shaida tsakanina da Isra'ilawa, cewa a kwana shida ni Ubangiji na yi sama da ƙasa, amma a rana ta bakwai na ajiye aiki, na huta.”’

18. Sa'ad da ya gama magana da Musa a kan Dutsen Sina'i, sai ya ba shi alluna biyu na shaida, allunan duwatsu rubatattu da yatsan Allah.

Karanta cikakken babi Fit 31