Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 30:24-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. da kashiya na shekel ɗari biyar bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, da moɗa ɗaya na man zaitun.

25. Da waɗannan za ku yi man keɓewa mai tsarki yadda mai yin turare yake yi, zai zama man keɓewa mai tsarki.

26. Za a shafa wa alfarwa ta sujada da akwatin alkawari wannan mai.

27. A kuma shafa wa teburin da kayayyakinsa, da alkukin da kayayyakinsa, da bagaden ƙona turare,

28. da bagaden hadaya ta ƙonawa da kayayyakinsa, da daron da gammonsa.

29. Ta haka za a tsarkake su domin su zama masu tsarki sosai. Duk abin da ya taɓa su zai tsarkaka.

30. Za ka zuba wa Haruna da ya'yansa maza mai, ka keɓe su domin su zama firistocina masu yi mini aiki.

31. Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Wannan mai, mai tsarki ne a gare ni domin keɓewa a dukan zamananku.

32. Ba za a shafa wa kowa ba, ba kuma za a yi wani mai irinsa ba, gama man tsattsarka ne, saboda haka zai kasance tsattsarka a gare ku.

33. Duk wanda ya yi wani irinsa ko kuwa ya shafa wa wani, za a raba shi da jama'arsa.”’

34. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ɗauki kayan yaji masu ƙanshi, su stakte, da onika, da galbanum tare da lubban. Su zama daidai wa daida.

35. Da waɗannan za a yi turare yadda mai yin turare yake yi, a sa masa gishiri, ya zama tsabtatacce, tsarkakakke.

Karanta cikakken babi Fit 30