Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 30:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji.

14. Duk wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar tun daga mai shekara ashirin ko fi, zai ba da wannan sadaka ga Ubangiji.

15. Lokacin da kuke ba da wannan sadaka ga Ubangiji saboda kafarar rayukanku, mai samu ba zai zarce ba, matalauci kuma ba zai ba da abin da ya gaza abin da aka ƙayyade ba.

16. Za ku karɓi kuɗin nan na kafara daga wurin Isra'ilawa, ku ajiye shi domin aiki a alfarwa ta sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar kansu.”

17. Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

18. “Sai ku yi daro da tagulla don wanka. Ku yi masa gammo da tagulla, ku ajiye shi tsakanin alfarwa ta sujada da bagaden, ku zuba ruwa a ciki.

19. A wurin ne Haruna da 'ya'yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu.

20. Sa'ad da suke shiga cikin alfarwa ta sujada ko sa'ad da suke kusatar bagade don su miƙa hadaya ta ƙonawa da wuta ga Ubangiji, sai su yi wanka don kada a kashe su.

Karanta cikakken babi Fit 30