Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 3:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya kuma ce, “Ni ne Allah na kakanninka, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah.

7. Ubangiji kuwa ya ce, “Na ga wahalar jama'ata waɗanda suke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu,

8. don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

9. Yanzu fa, ga shi, kukan jama'ar Isra'ila ya zo gare ni. Na kuma ga wahalar da Masarawa suke ba su.

10. Zo, in aike ka wurin Fir'auna domin ka fito da jama'ata, wato Isra'ilawa, daga cikin Masar.”

11. Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi gaban Fir'auna in fito da Isra'ilawa daga cikin Masar?”

12. Sai Allah ya ce, “Zan kasance tare da kai, wannan kuwa zai zama alama a gare ka, cewa ni ne na aike ka. Sa'ad da ka fito da jama'ar daga Masar, za ku bauta wa Allah a bisa dutsen nan.”

13. Sai Musa ya ce wa Allah, “Idan na je wurin Isra'ilawa na ce musu, ‘Allah na ubanninku ya aiko ni gare ku,’ idan sun ce mini, ‘Yaya sunansa?’ Me zan faɗa musu?”

14. Allah kuwa ya ce wa Musa, “NI INA NAN YADDA NAKE,” ya kuma ce, “Haka za ka faɗa wa Isra'ilawa, ‘NI NE ya aiko ni gare ku.”’

Karanta cikakken babi Fit 3