Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 3:4-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sa'ad da Ubangiji ya ga ya ratse don ya duba, sai Allah ya kira shi daga cikin kurmin, ya ce, “Musa, Musa.”Musa ya ce, “Ga ni.”

5. Allah kuwa ya ce, “Kada ka matso kusa, ka cire takalminka, gama wurin da kake tsaye, tsattsarka ne.”

6. Ya kuma ce, “Ni ne Allah na kakanninka, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah.

7. Ubangiji kuwa ya ce, “Na ga wahalar jama'ata waɗanda suke a Masar, na kuma ji kukansu da suke yi a kan shugabanninsu. Na san wahalarsu,

8. don haka na sauko in cece su daga hannun Masarawa, in fito da su daga cikin wannan ƙasa zuwa kyakkyawar ƙasa mai ba da yalwar abinci, wato ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

9. Yanzu fa, ga shi, kukan jama'ar Isra'ila ya zo gare ni. Na kuma ga wahalar da Masarawa suke ba su.

10. Zo, in aike ka wurin Fir'auna domin ka fito da jama'ata, wato Isra'ilawa, daga cikin Masar.”

Karanta cikakken babi Fit 3