Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 3:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wata rana, sa'ad da Musa yake kiwon garken surukinsa, Yetro, firist na Madayana, sai ya kai garken yammacin jeji, har ya zo Horeb, wato dutsen Allah.

2. A can mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba.

3. Musa kuwa ya ce, “Bari in ratse, in ga wannan abin banmamaki da ya sa kurmin bai ƙone ba.”

Karanta cikakken babi Fit 3