18. A jeri na biyu, a sa turkos, da saffir, da daimon.
19. A jeri na uku, a sa yakinta, da idon mage, da ametis.
20. A jeri na huɗu, a sa beril, da onis, da yasfa. Za a sa su cikin tsaiko na zinariya.
21. A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zana sunayen 'ya'yan Isra'ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zana sunayen kamar hatimi.
22. Ku kuma yi wa ƙyallen maƙalawa a ƙirji tukakkun sarƙoƙi na zinariya tsantsa.
23. Za ku yi ƙawanya biyu na zinariya, ku sa su a gefe biyu na ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
24. Ku sa tukakkun sarkoƙin nan biyu na zinariya a cikin ƙawanya biyu na zinariya da suke a gyaffan ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a haɗa su daga gaba a kafaɗun falmaran.
25. Za ku kuma sa sauran bakunan sarƙoƙin nan biyu a cikin tsaikuna, sa'an nan a sa shi a gaban kafaɗun falmaran.
26. Ku kuma yi waɗansu ƙawane na zinariya, a sa su a sauran kusurwoyi na ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a gefe na cikin da yake manne da falmaran.
27. Ku kuma yi waɗansu ƙawanya biyu na zinariya, a sa su a ƙashiyar kafaɗu biyu na falmaran daga gaba, a sama da abin ɗamaran nan.
28. Za su ɗaure ƙyallen maƙalawa a ƙirji a ƙawanensa haɗe da ƙawanen falmaran da shuɗiyar igiya domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji ya zauna bisa abin ɗamarar falmaran, don kuma kada ya yi sako-sako a bisa falmaran.