Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 27:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. A yi masa zankaye a kusurwoyinsa. Za ku haɗa zankayen da jikin bagaden. Za ku dalaye bagaden duka da tagulla.

3. Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla.

4. Za ku kuma yi wa bagaden raga da tagulla, sa'an nan ku sa wa ragar ƙawane a kusurwoyinta huɗu.

5. Za ku sa ragar a cikin bagaden a tsakiya.

6. Ku yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, sa'an nan ku dalaye su da tagulla.

7. Za a zura sandunan a ƙawanen da suke gyaffan bagade don ɗaukarsa.

Karanta cikakken babi Fit 27