Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 26:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.

2. Tsawon kowane labule zai zama kamu ashirin da takwas, fāɗinsa kuwa kamu huɗu. Labulen su zama daidai wa daida.

3. Labule biyar biyar, za a harhaɗa, a ɗinka.

4. Ku kuma yi wa labulen nan biyu hantuna na shuɗi a karbunsu na bisa.

5. Za ku yi wa kowane labule hantuna hamsin. Hantunan labulen nan biyu su yi daura da juna.

6. Za ku yi maɗauri guda hamsin da zinariya don a haɗa hantuna na labulen nan domin alfarwa ta zama ɗaya.

7. “Ku yi labule goma sha ɗaya da gashin awaki, da za ku rufe alfarwar da shi.

8. Tsawon kowanne zai zama kamu talatin, fāɗinsa kamu huɗu. Labulen za su zama daidai wa daida.

9. Za ku harhaɗa biyar ku ɗinka. Haka kuma za ku yi da sauran shidan. Ku ninka na shida riɓi biyu, ku yi labulen ƙofar alfarwa da shi.

10. Za ku kuma sa hantuna hamsin a karbun labulen daga bisa. Haka nan kuma za a sa hantuna hamsin a karbun ɗayan.

11. Sa'an nan ku yi maɗauri hamsin da tagulla, ku ɗaura hantunan da su don ku haɗa alfarwar ta zama ɗaya.

12. Ragowar rabin labulen da yake a bisa alfarwar, sai a bar shi yana reto a bayan alfarwar.

Karanta cikakken babi Fit 26