Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 24:2-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Musa ne kaɗai zai kusaci Ubangiji. Amma sauran kada su zo kusa, kada kuma jama'a su hau tare da shi.”

3. Musa ya tafi, ya faɗa wa jama'a dukan dokokin Ubangiji da ka'idodinsa, sai dukan jama'a suka amsa gaba ɗaya, suka ce, “Za mu kiyaye dukan dokokin da Ubangiji ya ba mu.”

4. Musa kuwa ya rubuta dukan dokokin Ubangiji. Kashegari da sassafe ya gina bagade a gindin dutsen, da kuma ginshiƙai goma sha biyu bisa ga yawan kabilai goma sha biyu na Isra'ila.

5. Ya kuma sa samarin Isra'ila su miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama, da bijimai ga Ubangiji.

6. Sai Musa ya zuba rabin jinin a tasa, sauran rabin jinin kuwa ya yayyafa a kan bagade.

7. Ya kuma ɗauki Littafin Alkawari, ya karanta wa jama'a, sai suka ce, “Za mu yi dukan abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi biyayya.”

8. Musa kuwa ya ɗauki jinin ya watsa wa jama'ar. Sa'an nan ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, wanda yake cikin dokokin nan duka.”

9. Musa ya haura tare da Haruna, da Nadab, da Abihu, da dattawan nan saba'in na Isra'ila.

10. Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.

11. Amma Ubangiji bai yi wa dattawan Isra'ila wani abu ba, ko da yake suka ga zatin Allah. Su kuma suka ci suka sha a gaban Allah.

12. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka hawo zuwa wurina a bisa dutsen, ka zauna har in ba ka allunan dutse da yake da dokoki da farillan da na rubuta don a koya musu.”

Karanta cikakken babi Fit 24