Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 23:27-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. “Zan aiki razanata a gabanku, in sa mutanen da za ku gamu da su su ruɗe. Zan sa maƙiyanku duka su ba ku baya, su sheƙa a guje.

28. Zan aiki zirnako a gabanku, su kore muku Hiwiyawa, da Kan'aniyawa, da Hittiyawa.

29. Ba a shekara guda zan kore muku su ba, don kada ƙasar ta zama kufai har namomin jeji su fi ƙarfinku.

30. Da kaɗan da kaɗan zan kore muku su, har yawanku ya kai yadda za ku mallaki ƙasar.

31. Zan yanka muku kan iyaka daga Bahar Maliya zuwa tekun Filistiyawa, daga jeji kuma zuwa Kogin Yufiretis. Gama zan ba da mazaunan ƙasar a hannunku, za ku kore su daga gabanku.

32. Kada ku ƙulla alkawari da su, ko da allolinsu.

33. Kada su zauna cikin ƙasarku domin kada su sa ku ku yi mini zunubi, ku bauta wa allolinsu, har abin kuwa ya zamar muku tarko.”

Karanta cikakken babi Fit 23