Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 22:7-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Idan mutum ya ba amininsa amanar kuɗi, ko amanar kadara, amma aka sace, in aka sami ɓarawon, a sa shi ya biya ninki biyu.

8. In kuwa ba a sami ɓarawon ba, sai a kawo maigidan a gaban Allah don a tabbatar babu hannunsa a cikin dukiyar amininsa.

9. “A kowane laifi na cin amana, ko sa ne, ko jaki, ko tunkiya, ko tufa, ko kowane ɓataccen abu, da abin da aka samu a hannun wani, in akwai jayayya, za a kawo mutumin nan a gaban Allah. Wanda Allah ya ce shi ne da laifi, sai ya biya wa ɗayan ninki biyu.

10. “In mutum ya bai wa amininsa amanar jaki, ko sa, ko tunkiya ko kowace irin dabba, amma dabbar ta mutu, ko ta yi rauni, ko ta ɓace, in ba shaida,

11. rantsuwa ce za ta raba tsakaninsu don a tabbatar babu hannunsa a dukiyar amininsa, mai dukiyar kuwa ya yarda da rantsuwar. Wanda aka bai wa amanar ba zai biya ba.

12. In dai sacewa aka yi, sai ya biya mai shi.

13. Idan kuwa naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shida. Ba zai yi ramuwar abin da naman jeji ya kashe ba.

14. “Idan mutum ya yi aron wani abu a wurin maƙwabcinsa, in abin ya yi rauni ko ya mutu, sa'ad da mai abin ba ya nan, lalle ne ya yi ramuwa.

15. Amma in mai abin yana wurin, wanda ya yi aro ba zai yi ramuwa ba. Idan kuwa jingina ce aka yi, kuɗin jinginar ne ramuwar.”

16. “Idan mutum ya rarrashi budurwa wadda ba a tashinta, har ya ɓata ta, sai ya biya sadaki, ya aure ta.

17. Amma idan mahaifinta bai yarda ya ba da ita gare shi ba, sai mutumin ya ba da sadaki daidai da abin da akan biya domin budurwa.

18. “Kada a bar mace mai sihiri ta rayu.

19. “Duk wanda ya kwana da dabba, lalle kashe shi za a yi.

20. “Wanda ya miƙa hadaya ga wani allah, ba ga Ubangiji ba, sai a hallaka shi ɗungum.

21. “Kada ku wulakanta baƙo ko ku zalunce shi, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

Karanta cikakken babi Fit 22