Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 22:13-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Idan kuwa naman jeji ne ya kashe ta, zai nuna gawar don shida. Ba zai yi ramuwar abin da naman jeji ya kashe ba.

14. “Idan mutum ya yi aron wani abu a wurin maƙwabcinsa, in abin ya yi rauni ko ya mutu, sa'ad da mai abin ba ya nan, lalle ne ya yi ramuwa.

15. Amma in mai abin yana wurin, wanda ya yi aro ba zai yi ramuwa ba. Idan kuwa jingina ce aka yi, kuɗin jinginar ne ramuwar.”

16. “Idan mutum ya rarrashi budurwa wadda ba a tashinta, har ya ɓata ta, sai ya biya sadaki, ya aure ta.

17. Amma idan mahaifinta bai yarda ya ba da ita gare shi ba, sai mutumin ya ba da sadaki daidai da abin da akan biya domin budurwa.

18. “Kada a bar mace mai sihiri ta rayu.

19. “Duk wanda ya kwana da dabba, lalle kashe shi za a yi.

20. “Wanda ya miƙa hadaya ga wani allah, ba ga Ubangiji ba, sai a hallaka shi ɗungum.

21. “Kada ku wulakanta baƙo ko ku zalunce shi, gama dā ku baƙi ne a ƙasar Masar.

22. Kada ku ci zalun marayu da gwauraye.

23. In kun tsananta musu, ba shakka za su yi kuka gare ni, ni kuma, hakika zan ji kukansu.

24. Zan husata, in sa a kashe ku cikin yaƙi, matanku, su ma, su zama gwauraye, 'ya'yanku kuwa su zama marayu.

25. “Idan kun ranta wa jama'ata matalauta da suke tsakaninku kuɗi, ba za ku zama musu kamar masu ba da rance da ruwa ba. Kada ku nemi ruwan kuɗin daga gare su.

26. In har wani ya karɓi rigar amininsa jingina, lalle ne ya mayar masa da ita kafin faɗuwar rana.

27. Gama wannan ne kaɗai mayafinsa, da shi zai rufe huntancinsa. Da me zai rufa ya yi barci? Zan amsa masa kuwa in ya yi kuka gare ni, gama cike nake da juyayi.

Karanta cikakken babi Fit 22