Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 22:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Idan mutum ya saci sa ko tunkiya, ya yanka ko ya sayar, zai biya shanu biyar a maimakon sa, tumaki huɗu maimakon tunkiya.

2. In aka iske ɓarawo yana cikin ƙoƙarin shiga ya yi sata, aka buge shi har ya mutu, to, ba za a nemi alhakin jininsa ga kowa ba,

3. sai dai ko in gari ya riga ya waye. Dole ɓarawon ya yi cikakkiyar ramuwa, in kuwa ba shi da abin biya, a sayar da shi a biya abin da ya satar.

4. In kuwa aka iske dabbar da ya satar a hannunsa da rai, ko sa, ko jaki, ko tunkiya, lalle ne ya biya riɓi biyu.

5. “In mutum ya kai dabbarsa kiwo a saura ko a garka, ya bar ta, ta yi ɓarna a gonar wani, ko a gonar inabin wani, sai a sa mai dabbar ya biya tara daga amfanin gonarsa mafi kyau duka.

6. “Idan wuta ta tashi a jeji ta ƙone tarin hatsi, ko hatsin da yake tsaye, ko gona, wanda ya sa wutar lalle ya biya cikakkiyar ramuwa.

Karanta cikakken babi Fit 22