Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 18:13-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Kashegari da Musa ya zauna garin yi wa jama'ar shari'a, mutane suka kekkewaye shi tun dage safiya har zuwa yamma.

14. Da surukin Musa ya ga yadda Musa yake fama da jama'a, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa jama'a? Don me kake zaune kai kaɗai, mutane kuwa na tsattsaye kewaye da kai, tun daga safe har zuwa maraice?”

15. Sai Musa ya ce wa surukinsa, “Mutane suna zuwa wurina ne domin su san faɗar Allah.

16. A sa'ad da suke da wata matsala sukan zo wurina, ni kuwa nakan daidaita tsakanin mutum da maƙwabcinsa, nakan kuma koya musu dokokin Allah da umarnansa.”

17. Amma surukin Musa ya ce, “Abin nan da kake yi ba daidai ba ne.

18. Kai da jama'an nan da suke tare da kai za ku rafke, saboda abin da kake yi ya fi ƙarfinka, kai kaɗai ba za ka iya ba.

19. Yanzu sai ka saurari maganata, zan ba ka shawara, Allah kuwa ya kasance tare da kai. Za ka wakilci jama'a a gaban Allah, ka kai matsalolinsu gare shi.

20. Ka koya musu dokokin da umarnan, ka nuna musu hanyar da ya kamata su yi.

21. Ka kuma zaɓa daga cikin jama'a isassun mutane, masu tsoron Allah, amintattu, waɗanda suke ƙyamar cin hanci. Ka naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.

22. Za su yi wa mutane shari'a koyaushe, amma kowace babbar matsala sai su kawo maka, ƙaramar matsala kuwa su yanke da kansu. Da haka za su ɗauki nauyin jama'a tare da kai don ya yi maka sauƙi.

23. In ka bi wannan shawara, in kuma Allah ya umarce ka da yin haka, za ka iya ɗaukar nawayar jama'ar. Mutane duka kuwa za su yi zamansu lafiya.”

24. Musa kuwa ya saurari maganar surukinsa, ya yi abin da ya ce duka.

25. Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra'ilawa ya naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.

26. Suka yi ta yi wa jama'a duka shari'a kullayaumin, amma matsaloli masu wuya sukan kawo wa Musa, ƙananan kuwa sukan yanke da kansu.

Karanta cikakken babi Fit 18