Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 17:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan taron jama'ar Isra'ila suka tashi daga jejin Sin, suna tafiya daga zango zuwa zango bisa ga umarnin Ubangiji. Suka yi zango a Refidim, amma ba ruwan da jama'a za su sha.

2. Domin haka jama'a suka zargi Musa suka ce, “Ba mu ruwa, mu sha.”Musa ya amsa musu ya ce, “Don me kuke zargina? Don me kuke gwada Ubangiji?”

3. Amma jama'a suna fama da ƙishirwa, suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, “Don me ka fito da mu daga Masar? Ashe, domin ka kashe mu ne, da mu, da 'ya'yanmu, da dabbobinmu da ƙishi?”

4. Sai Musa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Me zan yi wa jama'an nan? Ga shi, saura kaɗan su jajjefe ni da duwatsu.”

Karanta cikakken babi Fit 17