Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 16:25-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Sai Musa ya ce, “Ita za ku ci yau, gama yau Asabar ce ga Ubangiji. Yau ba za ku same ta a saura ba.

26. Kwana shida za ku tattara ta, amma a rana ta bakwai wadda take asabar, ba za a iske kome ba.”

27. Amma a rana ta bakwai ɗin waɗansu mutane suka tafi don su tattara, ba su kuwa sami kome ba.

28. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi kiyaye dokokina da umarnaina?

29. Lura fa, Ubangiji ne ya ba ku ranar Asabar, domin haka a rana ta shida yakan ba ku abinci na kwana biyu. Kowanne ya yi zamansa a inda yake. Kada kowa ya bar inda yake a rana ta bakwai ɗin.”

30. Sai jama'a suka huta a rana ta bakwai.

31. Isra'ilawa kuwa suka sa wa wannan abinci suna, Manna. Manna wata irin tsaba ce kamar farin riɗi. Ɗanɗanarta kuwa kamar waina ce da aka yi da zuma.

32. Sai Musa ya ce, “Ubangiji ya umarta a cika mudu da ita, a adana ta dukan zamananku domin kowane zamani a ga irin abincin da ya ciyar da ku cikin jeji lokacin da ya fito da ku daga ƙasar Masar.”

33. Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki tukunya, ka zuba mudu guda na manna a ciki, ka ajiye a gaban Ubangiji, a adana har dukan zamananku.”

34. Kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, haka Haruna ya ajiye ta a gaban akwatin alkawari domin kiyayewa.

35. Shekara arba'in Isra'ilawa suka yi suna cin manna, har suka kai ƙasar da take da mutane, suka ci manna, har zuwa kan iyakar ƙasar Kan'ana.

36. Mudu ɗaya humushin garwa ɗaya ta gari.

Karanta cikakken babi Fit 16