Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 16:18-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Amma da aka auna da mudu, ta waɗanda suka zarce ba ta yi saura ba, ta waɗanda ba su kai ba, ba ta gaza ba. Kowane mutum ya tattara daidai cinsa.

19. Musa ya ce musu, “Kada wani ya ci, ya bar saura har safiya.”

20. Amma waɗansu ba su kasa kunne ga Musa ba, suka bar saura, har ta kwana, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su.

21. Kowace safiya sukan tattara ta, kowa gwargwadon cinsa, amma da rana ta yi zafi sai manna ɗin ta narke.

22. A kan rana ta shida suka tattara biyu ɗin abin da suka saba, kowane mutum mudu biyu biyu. Sai shugabannin taron suka zo suka faɗa wa Musa.

23. Shi kuwa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya umarta, ‘Gobe ranar hutawa ce ta saduda, Asabar ce, tsattsarka ga Ubangiji. Ku toya abin da za ku toya, ku kuma dafa abin da za ku dafa. Abin da kuka ci kuka rage, ku ajiye don gobe.”’

24. Suka ajiye har gobe kamar yadda Musa ya umarta, amma ba ta yi ɗoyi ba, ba ta kuwa yi tsutsotsi ba.

25. Sai Musa ya ce, “Ita za ku ci yau, gama yau Asabar ce ga Ubangiji. Yau ba za ku same ta a saura ba.

Karanta cikakken babi Fit 16