Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 13:2-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Keɓe mini 'ya'yan fari maza duka. Kowane ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa cikin Isra'ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”

3. Musa ya ce wa jama'a, “Ku kiyaye wannan rana da kuka fito daga Masar, daga gidan bauta, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fitar da ku daga wurin. Daɗai, ba za ku ci abinci mai yisti ba.

4. A wannan rana kuka fita, wato a watan Abib.

5. Sai ku kiyaye wannan farilla a wannan wata sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, wadda ya rantse wa kakanninku zai ba ku, wato ƙasar da take ba da yalwar abinci.

6. Sai ku riƙa cin abinci marar yisti har kwana bakwai, amma a rana ta bakwai za ku yi idi ga Ubangiji.

7. Abinci marar yisti za a ci har kwana bakwai. Kada a ga wani da abinci mai yisti, ko kuma yisti ɗin kansa, a ko'ina a wurarenku.

8. A wannan rana kowa zai sanar wa ɗansa cewa abubuwan nan da muke yi, muna yi ne don tunawa da abin da Ubangiji ya yi mana sa'ad da ya fitar da mu daga Masar.

9. Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari'ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar.

10. Sai ku kiyaye farillan nan kowace shekara a lokacinta.”

11. “Sa'ad da Ubangiji ya kai ku ƙasar Kan'aniyawa wadda zai ba ku kamar yadda ya rantse muku, ku da kakanninku,

12. sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Kowane ɗan farin dabbarku na Ubangiji ne.

13. Amma a fanshi kowane ɗan farin jakinku da ɗan rago. Idan kuwa ba za ku fanshe shi ba, sai ku karye wuyansa. Kowane ɗan farin 'ya'yanku, sai ku fanshe shi.

14. In wata rana 'ya'yanku suka tambaye ku cewa, ‘Ina ma'anar wannan?’ Sai ku ce musu, ‘Da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar, daga gidan bauta.

15. Gama sa'ad da Fir'auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, Ubangiji kuwa ya kashe dukan 'ya'yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba gaba ɗaya. Domin haka muke yin hadaya ga Ubangiji da 'ya'yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma mukan fanshi dukan 'ya'yan farinmu, maza.’

16. Al'amarin nan kuwa zai zama matuni kamar alama a hannunku ko a goshinku, gama da iko Ubangiji ya fisshe mu daga Masar.”

17. Da Fir'auna ya bar jama'a su tafi, Allah bai bi da su ta hanyar ƙasar Filistiyawa ba, ko da yake wannan hanya ta fi kusa, gama Allah ya ce, “Don kada jama'a su sāke tunaninsu sa'ad da suka ga yaƙi, su koma Masar.”

Karanta cikakken babi Fit 13