Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 10:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Za su cika fādarka, da dukan gidajen fādawanka, da na dukan Masarawa. Iyayenka da kakanninka ba su taɓa ganin irin faran nan ba, tun daga ran da suke ƙasar, har wa yau.”’ Sai ya juya ya fita daga gaban Fir'auna.

7. Fādawan Fir'auna kuwa suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai riƙa jawo mana masifa? Ka saki mutanen, su fita su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Ashe, har yanzu ba ka sani Masar ta lalace ba?”

8. Aka komar da Musa da Haruna gaban Fir'auna. Sai Fir'auna ya ce musu, “Ku tafi ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?”

9. Musa ya amsa, “Da samarinmu, da tsofaffinmu za mu tafi, da 'ya'yanmu mata da maza za su fita tare da mu, da kuma garkunanmu da shanunmu, gama wajibi ne mu yi idi a gaban Ubangiji.

10. Fir'auna ya ce musu, “To, Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba, gama kuna da niyyar mugunta a zuciyarku.

Karanta cikakken babi Fit 10