Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 10:16-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Fir'auna ya aika da gaggawa a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku.

17. Amma ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma roƙar mini Ubangiji Allahnku ya ɗauke mini wannan mutuwa.”

18. Sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna, ya tafi ya roƙi Ubangiji.

19. Ubangiji kuwa ya sa iska mai ƙarfi ta huro daga wajen yamma, ta kwashi farar, ta zuba ta a Bahar Maliya. Ko fara guda ba ta ragu a cikin iyakar Masar ba.

20. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna, Fir'auna kuwa ya ƙi sakin Isra'ilawa.

21. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama, domin a yi duhu cikin ƙasar Masar, irin duhun da za a iya taɓawa.”

22. Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuwa yi duhu baƙi ƙirin har kwana uku a dukan ƙasar Masar.

23. Mutum bai iya ganin ɗan'uwansa ba, ba kuma mutumin da ya iya fita gidansa har kwana uku. Amma akwai haske inda Isra'ilawa suke zaune.

24. Fir'auna ya kirawo Musa da Haruna ya ce musu, “Ku tafi ku bauta wa Ubangiji, sai dai ku bar tumakinku, da awakinku, da shanunku a nan, amma ku ku tafi da 'ya'yanku.”

25. Musa kuwa ya ce, “In haka ne, kai ka ba mu abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu hadayu da su.

26. Don haka sai mu tafi da dabbobinmu, ko kofato ba za a bari a baya ba, gama daga cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.”

27. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir'auna har bai yarda ya sake su ba.

28. Fir'auna ma ya ce wa Musa, “Tafi, ka ba ni wuri, ka mai da hankali fa, kada in ƙara ganinka, gama ran da na sāke ganinka ran nan kā mutu.”

29. Sai Musa ya amsa ya ce, “Haka nan ne kuwa, ba zan ƙara ganin fuskarka ba.”

Karanta cikakken babi Fit 10