Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 1:11-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.

12. Amma ko da yake Masarawa sun ƙara tsananta musu, duk da haka sai suka ƙara ƙaruwa, suna ta yaɗuwa. Masarawa kuwa suka tsorata saboda Isra'ilawa.

13. Suka kuma tilasta wa Isra'ilawa su yi ta aiki mai tsanani.

14. Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu.

15. Sarkin Masar ya ce wa ungozomar Ibraniyawa, Shifra da Fu'a,

16. “Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”

17. Amma da yake ungozomar masu tsoron Allah ne, ba su yi yadda Sarkin Masar ya umarce su ba, amma suka bar 'ya'ya maza da rai.

18. Don haka Sarkin Masar ya kirawo ungozomar, ya ce musu, “Me ya sa kuka bar 'ya'ya maza da rai?”

19. Ungozomar suka ce wa Fir'auna, “Domin matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gama su masu ƙwazo ne, sukan haihu tun ungozomar ba su kai wurinsu ba.”

20. Allah kuwa ya yi wa ungozoman nan alheri. Mutanen suka riɓanya, suka ƙasaita ƙwarai.

Karanta cikakken babi Fit 1