Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fit 1:11-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.

12. Amma ko da yake Masarawa sun ƙara tsananta musu, duk da haka sai suka ƙara ƙaruwa, suna ta yaɗuwa. Masarawa kuwa suka tsorata saboda Isra'ilawa.

13. Suka kuma tilasta wa Isra'ilawa su yi ta aiki mai tsanani.

14. Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu.

15. Sarkin Masar ya ce wa ungozomar Ibraniyawa, Shifra da Fu'a,

16. “Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”

Karanta cikakken babi Fit 1