Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 9:20-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Nuhu shi ya fara noma, ya yi gonar inabi.

21. Ya sha daga cikin ruwan inabin ya kuwa bugu, ya kwanta tsirara a cikin alfarwarsa.

22. Sai Ham, mahaifin Kan'ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya faɗa wa 'yan'uwansa biyu waɗanda suke waje.

23. Sai Shem da Yafet suka ɗauki riga, suka ɗibiya bisa kafaɗunsu, suka yi tafiya da baya da baya suka rufa tsiraicin mahaifinsu, suka juya fuskokinsu, ba su kuwa ga tsiraicin mahaifinsu ba.

24. Sa'ad da ruwan inabin ya sau Nuhu, ya san abin da ƙaramin ɗansa ya yi masa.

25. Sai ya ce, “La'ananne ne Kan'ana, bawan bayi zai zama ga 'yan'uwansa.”

26. Ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahna, ya sa wa Shem albarka, Kan'ana kuwa ya bauta masa.

27. Allah ya sa Yafet ya yawaita, ya sa ya zauna a alfarwan Shem, Kan'ana kuwa ya bauta masa.”

28. Bayan Ruwan Tsufana, Nuhu ya yi shekara ɗari uku da hamsin.

29. Shekarun Nuhu duka ɗari tara da hamsin ne, ya rasu.

Karanta cikakken babi Far 9