Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 50:23-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Yusufu fa ya ga 'ya'yan Ifraimu har tsara ta uku, aka kuma haifi 'ya'yan Makir ɗan Manassa, aka karɓe su cikin iyalin Yusufu.

24. Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ina gab da mutuwa, amma lalle Allah zai ziyarce ku, zai kuwa haurar da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”

25. Sa'an nan Yusufu ya rantse wa 'ya'yan Isra'ila da cewa, “Hakika Allah zai ziyarce ku, ku kuma sai ku haura da ƙasusuwana daga nan.”

26. Yusufu ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Sai suka shafe shi da maganin hana ruɓa. Aka kuwa sa shi a akwatin gawa cikin Masar.

Karanta cikakken babi Far 50