Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 49:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba,Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsuba,Gama cikin fushinsu suka kashemutane,Cikin gangancinsu kuma sukagurgunta bijimai.

7. La'ananne ne fushinsu domin maitsanani ne,Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce.Zan warwatsa su cikin dukan ƙasarYakubu,In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.

8. “Yahuza, 'yan'uwanka za su yabeka,Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka,'Yan'uwanka za su rusuna agabanka.

9. Yahuza ɗan zaki ne,Ya kashe ganima sa'an nan ya komowurin ɓuyarsa.Yahuza kamar zaki yake,Yakan kwanta a miƙe,Ba mai ƙarfin halin da zai tsokaneshi.

10. Yana riƙe da sandan mulkinsa,Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa,Har Shilo ya zo.Zai mallaki dukan jama'o'i.

11. Zai ɗaure aholakinsa a kurangarinabi,A kuranga mafi kyau,Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi,Ruwan inabi ja wur kamar jini.

12. Idanunsa za su yi ja wur saboda shanruwan inabi,Haƙoransa kuma su yi fari fatsaboda shan madara.

13. “Zabaluna zai zauna a gefen teku,Zai zama tashar jiragen ruwa,Kan iyakarsa kuma zai kai harSidon.

14. “Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa,Ya kwanta a miƙe tsakaninjakunkunan shimfiɗa.

15. Saboda ya ga wurin hutawa ne maikyau,Ƙasar kuma mai kyau ce,Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa dominɗaukar kaya,Ya zama bawa, yana yin aiki maiwuya.

16. “Dan zai zama mai mulki gamutanensaKamar ɗaya daga cikin kabilanIsra'ila.

17. Dan zai zama maciji a gefen hanya,Zai zama kububuwa a gefen turba,Mai saran diddigen dokiDon mahayin ya fāɗi da baya.

Karanta cikakken babi Far 49