Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Faɗar Yakubu a kan 'Ya'yansa

1. Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa.

2. “Ku taru ku ji, ya ku 'ya'yanYakubu, maza,Ku kuma kasa kunne ga Isra'ilamahaifinku.

3. “Ra'ubainu, kai ɗan farinane, ƙarfina,Ɗan balagata, isasshe kuma, mafiƙarfi duka cikin 'ya'yana.

4. Kamar ambaliyar ruwa mai fushikake,Amma ba za ka zama mafi darajaba,Domin ka hau gadon mahaifinka,Sa'an nan ka ƙazantar da shi.

5. “Saminu da Lawi 'yan'uwa ne,Suka mori takubansu cikin ta dahankali.

6. Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba,Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsuba,Gama cikin fushinsu suka kashemutane,Cikin gangancinsu kuma sukagurgunta bijimai.

7. La'ananne ne fushinsu domin maitsanani ne,Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce.Zan warwatsa su cikin dukan ƙasarYakubu,In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.

8. “Yahuza, 'yan'uwanka za su yabeka,Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka,'Yan'uwanka za su rusuna agabanka.

9. Yahuza ɗan zaki ne,Ya kashe ganima sa'an nan ya komowurin ɓuyarsa.Yahuza kamar zaki yake,Yakan kwanta a miƙe,Ba mai ƙarfin halin da zai tsokaneshi.

10. Yana riƙe da sandan mulkinsa,Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa,Har Shilo ya zo.Zai mallaki dukan jama'o'i.

11. Zai ɗaure aholakinsa a kurangarinabi,A kuranga mafi kyau,Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi,Ruwan inabi ja wur kamar jini.

12. Idanunsa za su yi ja wur saboda shanruwan inabi,Haƙoransa kuma su yi fari fatsaboda shan madara.

13. “Zabaluna zai zauna a gefen teku,Zai zama tashar jiragen ruwa,Kan iyakarsa kuma zai kai harSidon.

14. “Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa,Ya kwanta a miƙe tsakaninjakunkunan shimfiɗa.

15. Saboda ya ga wurin hutawa ne maikyau,Ƙasar kuma mai kyau ce,Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa dominɗaukar kaya,Ya zama bawa, yana yin aiki maiwuya.

16. “Dan zai zama mai mulki gamutanensaKamar ɗaya daga cikin kabilanIsra'ila.

17. Dan zai zama maciji a gefen hanya,Zai zama kububuwa a gefen turba,Mai saran diddigen dokiDon mahayin ya fāɗi da baya.

18. Ina zuba ido ga cetonka, yaUbangiji.

19. “Gad, 'yan fashi za su kai masa hari,Shi kuwa zai runtume su.

20. “Ashiru, ƙasarsa za ta ba da amfanimai yawa,Zai kuma yi tanadin abincin da yadace da sarki.

21. “Naftali sakakkiyar barewa ce,Mai haihuwar kyawawan 'ya'ya.

22. “Yusufu jakin jeji ne,Jakin jeji a gefen maɓuɓɓugaAholakan jeji a gefen tuddai.

23. Maharba suka tasar masa ba tausayiSuka fafare shi da kwari da baka.

24. Duk da haka bakunansu sunkakkarye.Damatsansu sun yayyageTa wurin ikon Allah Mai Girma naYakubu,Makiyayi, Dutse na Isra'ila.

25. Ta wurin Allah na mahaifinka wandazai taimake ka,Ta wurin Allah Mai Iko Dukkawanda zai sa maka albarkaAlbarkun ruwan sama daga bisa,Da na zurfafa daga ƙarƙashinƙasa,Da albarkun mama da na mahaifa.

26. Albarkun hatsi da na gariAlbarkun daɗaɗɗun duwatsu,Abubuwan jin daɗi na madawwamantuddai,Allah ya sa su zauna a kan Yusufu,Da a goshin wanda aka raba shi da'yan'uwansa.

27. “Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa,Da safe yakan cinye abin da yakaso,Da maraice kuma yakan raba abin daya kamo.”

28. Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.

Rasuwar Yakubu da Jana'izarsa

29. Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte,

30. a cikin kogon da yake a Makfela, gabashin Mamre, a ƙasar Kan'ana, wanda Ibrahim ya saya duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.

31. A can aka binne Ibrahim da Saratu matarsa. A can kuma suka binne Ishaku da Rifkatu matarsa. A can kuma na binne Lai'atu.

32. Da saurar da kogon da yake cikinta, an saye su daga Hittiyawa.”

33. Sa'ad da Yakubu ya gama yi wa 'ya'yansa maza wasiyya, sai ya hau da ƙafafunsa bisa kan gado, Ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.