Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 49:17-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Dan zai zama maciji a gefen hanya,Zai zama kububuwa a gefen turba,Mai saran diddigen dokiDon mahayin ya fāɗi da baya.

18. Ina zuba ido ga cetonka, yaUbangiji.

19. “Gad, 'yan fashi za su kai masa hari,Shi kuwa zai runtume su.

20. “Ashiru, ƙasarsa za ta ba da amfanimai yawa,Zai kuma yi tanadin abincin da yadace da sarki.

21. “Naftali sakakkiyar barewa ce,Mai haihuwar kyawawan 'ya'ya.

22. “Yusufu jakin jeji ne,Jakin jeji a gefen maɓuɓɓugaAholakan jeji a gefen tuddai.

23. Maharba suka tasar masa ba tausayiSuka fafare shi da kwari da baka.

24. Duk da haka bakunansu sunkakkarye.Damatsansu sun yayyageTa wurin ikon Allah Mai Girma naYakubu,Makiyayi, Dutse na Isra'ila.

25. Ta wurin Allah na mahaifinka wandazai taimake ka,Ta wurin Allah Mai Iko Dukkawanda zai sa maka albarkaAlbarkun ruwan sama daga bisa,Da na zurfafa daga ƙarƙashinƙasa,Da albarkun mama da na mahaifa.

26. Albarkun hatsi da na gariAlbarkun daɗaɗɗun duwatsu,Abubuwan jin daɗi na madawwamantuddai,Allah ya sa su zauna a kan Yusufu,Da a goshin wanda aka raba shi da'yan'uwansa.

27. “Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa,Da safe yakan cinye abin da yakaso,Da maraice kuma yakan raba abin daya kamo.”

Karanta cikakken babi Far 49