Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 48:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Yanzu fa, idanun Isra'ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su.

11. Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ban yi zaton zan ga fuskarka ba, ga shi kuwa, Allah ya sa na gani har da na 'ya'yanka.”

12. Yusufu ya kawar da su daga gwiwoyin Isra'ila, ya sunkuyar da fuskarsa har ƙasa a gabansa.

13. Yusufu ya ɗauki su biyu ɗin, Ifraimu a hannunsa na dama zuwa hannun hagun Isra'ila, Manassa kuma a hannunsa na hagu zuwa dama na Isra'ila, ya kawo su kusa da shi.

14. Isra'ila ya miƙa hannunsa na dama, ya ɗora bisa kan Ifraimu wanda yake ƙarami, hannunsa na hagu kuma bisa kan Manassa, yana harɗe da hannuwansa, gama Manassa shi ne ɗan fari.

15. Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce,“Allah na Ibrahim da Ishaku,Iyayena da suka yi tafiyarsu agabansa,Allah da ya bi da niDukan raina har wa yau, ya sa musualbarka.

16. Mala'ikan da ya fanshe niDaga dukan mugunta,Ya sa wa samarin albarka,Bari a dinga ambatarsu da sunana,Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena,Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zamataron jama'a a tsakiyar duniya.”

17. Sa'ad da Yusufu ya ga mahaifinsa ya ɗora hannun damansa a bisa kan Ifraimu, ransa bai so ba, ya ɗauke hannun mahaifinsa, domin ya kawar da shi daga kan Ifraimu zuwa kan Manassa.

Karanta cikakken babi Far 48