Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 46:23-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Hushim shi ne ɗan Dan.

24. 'Ya'yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum.

25. Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa 'yarsa Rahila.

26. Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan 'ya'yansa, su mutum sittin da shida ne.

27. 'Ya'yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba'in.

28. Isra'ila kuwa ya aiki Yahuza ya yi gaba zuwa wurin Yusufu ya faɗa masa ya sadu da shi a nuna masa Goshen. Da suka zo ƙasar Goshen,

29. sai Yusufu ya kintsa karusarsa ya haura zuwa Goshen don ya taryi Isra'ila, mahaifinsa. Nan da nan da isowarsa wurinsa, ya rungume shi, ya jima yana ta kuka a kafaɗarsa.

30. Isra'ila ya ce wa Yusufu, “To, bari in mutu yanzu, tun da na ga fuskarka na sani kuma kana da rai har yanzu.”

31. Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa da iyalin gidan mahaifinsa, “Zan tafi in faɗa wa Fir'auna, in ce masa, ‘'yan'uwana da iyalin gidan mahaifina, waɗanda dā yake a ƙasar Kan'ana, sun zo wurina,)

Karanta cikakken babi Far 46