Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 46:19-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. 'Ya'ya maza, na Rahila, matar Yakubu, su ne Yusufu da Biliyaminu.

20. Asenat 'yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusufu Manassa da Ifraimu a ƙasar Masar.

21. 'Ya'yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na'aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar.

22. Waɗannan su goma sha huɗu su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Rahila.

23. Hushim shi ne ɗan Dan.

24. 'Ya'yan Naftali, maza, su ne Yazeyel, da Guni, da Yezer, da Shallum.

25. Waɗannan su bakwai, su ne zuriyar Yakubu, maza, na wajen Bilha, wadda Laban ya bai wa 'yarsa Rahila.

26. Mutanen Yakubu dukka da suka shiga Masar, waɗanda suke zuriyarsa ne, banda matan 'ya'yansa, su mutum sittin da shida ne.

27. 'Ya'yan Yusufu, maza, waɗanda aka haifa masa a Masar su biyu ne. Dukkan mutane na gidan Yakubu da suka zo Masar su saba'in.

28. Isra'ila kuwa ya aiki Yahuza ya yi gaba zuwa wurin Yusufu ya faɗa masa ya sadu da shi a nuna masa Goshen. Da suka zo ƙasar Goshen,

29. sai Yusufu ya kintsa karusarsa ya haura zuwa Goshen don ya taryi Isra'ila, mahaifinsa. Nan da nan da isowarsa wurinsa, ya rungume shi, ya jima yana ta kuka a kafaɗarsa.

30. Isra'ila ya ce wa Yusufu, “To, bari in mutu yanzu, tun da na ga fuskarka na sani kuma kana da rai har yanzu.”

31. Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa da iyalin gidan mahaifinsa, “Zan tafi in faɗa wa Fir'auna, in ce masa, ‘'yan'uwana da iyalin gidan mahaifina, waɗanda dā yake a ƙasar Kan'ana, sun zo wurina,)

32. mutanen kuwa makiyaya ne, sun kuwa zo da garkunansu na awaki da na tumaki, da garkunansu na shanu, da dukkan abin da suke da shi.’

Karanta cikakken babi Far 46