Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 45:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yusufu ya kasa daurewa a gaban dukan waɗanda suke a tsaye kusa da shi, sai ya ta da murya ya ce, “Kowa ya ba mu wuri.” Saboda haka ba mutumin da ya tsaya a wurin sa'ad da Yusufu ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa.

2. Ya yi kuka da ƙarfi, har Masarawa suka ji, labarin kuwa ya kai gidan Fir'auna.

3. Yusufu kuwa ya ce wa 'yan'uwansa, “Ni ne Yusufu. Mahaifina yana da rai har yanzu?” Amma 'yan'uwansa ba su iya ba shi amsa ba, gama sun firgita a gabansa.

4. Yusufu ya ce wa 'yan'uwansa. “Ku matso kusa da ni, ina roƙonku.” Suka matso kusa. Sai ya ce, “Ni ne ɗan'uwanku, Yusufu, wanda kuka sayar zuwa Masar.

5. Yanzu fa, kada ku damu ko kuwa ku ji haushin kanku domin kun sayar da ni a nan, gama Allah ne ya aike ni a gabanku don in ceci rai.

6. Gama shekara biyu ke nan da ake yunwa a ƙasar, amma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.

7. Allah kuwa ya aike ni a gabanku, domin in cetar muku da ringi a duniya, in kuma rayar muku kuɓutattu masu yawa.

8. Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir'auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka.

Karanta cikakken babi Far 45