Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 43:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sa'ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ɗan abinci.”

3. Amma Yahuza ya ce masa, “Mutumin fa, ya yi mana faɗakarwa sosai, ya ce, ‘Idan ba tare da autanku kuka zo ba, ba za ku ga fuskata ba.’

4. In za ka yarda ka aiki ɗan'uwanmu tare da mu, sai mu gangara mu sayo muku abinci.

5. Amma idan ba haka ba, ba za mu tafi ba, gama mutumin ya ce mana, ‘Ba za ku ga fuskata ba idan ba ku zo tare da ɗan'uwanku ba.’ ”

6. Sai Isra'ila ya ce, “Don me kuka cuce ni, da kuka faɗa wa mutumin nan, kuna da wani ɗan'uwa?”

7. Suka amsa, “Ai, mutumin ne ya yi ta tambayar labarinmu da na danginmu, yana cewa, ‘Mahaifinku yana da rai har yanzu? Kuna kuma da wani ɗan'uwa?’ Abin da muka faɗa masa amsoshi ne na waɗannan tambayoyi. Ta ƙaƙa za mu iya sani zai ce, ‘Ku zo da ɗan'uwanku’?”

8. Sai Yahuza ya ce wa Isra'ila, mahaifinsu, “Ka sa saurayin a hannuna, mu tashi mu tafi, mu sami abinci mu rayu, kada mu mutu, da mu da kai da ƙanananmu.

9. Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada,

10. gama da ba don mun yi jinkiri ba, da yanzu, ai, mun yi sawu biyu.”

Karanta cikakken babi Far 43