Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 42:9-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”

10. Suka ce masa, “A'a, shugabanmu, domin sayen abinci bayinka suka zo.

11. Mu duka 'ya'yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.”

12. Yusufu ya ce musu, “A'a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.”

13. Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”

14. Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku.

15. Ta haka za a jarraba ku, da ran Fir'auna, ba za ku fita daga nan wurin ba, sai autanku ya zo nan.

16. Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan'uwanku, amma ku, za a tsare ku, don a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya cikinku, idan ba haka ba kuwa, da ran Fir'auna, lalle ku magewaya ne.”

17. Sai ya tura su cikin waƙafi har kwana uku.

18. A kan rana ta uku, Yusufu ya ce musu, “Abin da za ku yi in bar ku da rai ke nan, gama ina tsoron Allah,

19. sai ku bar ɗan'uwanku ɗaya a tsare a inda aka kulle ku. Idan amintattu ne ku, sauran kuwa su tafi su kai hatsi ga iyalanku mayunwata,

20. sa'an nan su kawo mini autanku. Ta haka za a tabbatar da maganarku, har a bar ku da rai.” Haka kuwa suka yi.

21. Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan'uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa'ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.”

22. Sai Ra'ubainu ya amsa musu, “Ashe, dā ma ban faɗa muku kada ku cuci yaron ba? Amma ba ku saurara ba. To, ga shi fa, ana neman hakkinsa yanzu.

23. Ba su sani ba, ashe, Yusufu yana jinsu, domin akwai tafinta a tsakaninsu.

24. Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.

25. Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu.

Karanta cikakken babi Far 42