Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

'Yan'uwan Yusufu sun Zo Masar Sayen Abinci

1. A sa'ad da Yakubu ya ji akwai hatsi a Masar, sai ya ce wa 'ya'yansa maza, “Me ya sa kuke zuba wa juna ido?

2. Ga shi kuwa, na ji akwai hatsi a Masar, ku gangara ku sayo mana hatsi a can domin mu rayu, kada mu mutu.”

3. Don haka 'yan'uwan Yusufu su goma suka gangara su sayo hatsi a Masar.

4. Amma Yakubu bai aiki Biliyaminu ɗan'uwan Yusufu tare da 'yan'uwansa ba, gama ya ce, “Kada wata ɓarna ta same shi.”

5. Haka nan 'ya'yan Isra'ila maza suka zo su sayi hatsi tare da sauran matafiya, gama ana yunwa a ƙasar Kan'ana.

6. Yanzu fa, Yusufu shi ne mai mulkin ƙasar, shi ne kuwa mai sayar wa jama'ar ƙasar duka. 'Yan'uwan Yusufu suka zo suka sunkuya har ƙasa a gabansa.

7. Da Yusufu ya ga 'yan'uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?”Suka ce, “Daga ƙasar Kan'ana muka zo sayen abinci.”

8. Yusufu kuwa ya gane da 'yan'uwansa amma su ba su gane shi ba.

9. Sai Yusufu ya tuna da mafarkan da ya yi a kansu, ya ce musu, “Ku magewaya ne, zuwa kuka yi domin ku leƙi asirin ƙasar.”

10. Suka ce masa, “A'a, shugabanmu, domin sayen abinci bayinka suka zo.

11. Mu duka 'ya'yan mutum guda ne, amintattu kuma, bayinka ba magewaya ba ne.”

12. Yusufu ya ce musu, “A'a! Ku dai kun zo ku ga inda ƙasarmu yake da rashin ƙarfi.”

13. Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”

14. Amma Yusufu ya ce musu, “Ai, kamar dai yadda na faɗa muku, magewaya ne ku.

15. Ta haka za a jarraba ku, da ran Fir'auna, ba za ku fita daga nan wurin ba, sai autanku ya zo nan.

16. Ku aiki ɗaya daga cikinku ya kawo ɗan'uwanku, amma ku, za a tsare ku, don a tabbatar da maganarku, ko akwai gaskiya cikinku, idan ba haka ba kuwa, da ran Fir'auna, lalle ku magewaya ne.”

17. Sai ya tura su cikin waƙafi har kwana uku.

18. A kan rana ta uku, Yusufu ya ce musu, “Abin da za ku yi in bar ku da rai ke nan, gama ina tsoron Allah,

19. sai ku bar ɗan'uwanku ɗaya a tsare a inda aka kulle ku. Idan amintattu ne ku, sauran kuwa su tafi su kai hatsi ga iyalanku mayunwata,

20. sa'an nan su kawo mini autanku. Ta haka za a tabbatar da maganarku, har a bar ku da rai.” Haka kuwa suka yi.

21. Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan'uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa'ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.”

22. Sai Ra'ubainu ya amsa musu, “Ashe, dā ma ban faɗa muku kada ku cuci yaron ba? Amma ba ku saurara ba. To, ga shi fa, ana neman hakkinsa yanzu.

23. Ba su sani ba, ashe, Yusufu yana jinsu, domin akwai tafinta a tsakaninsu.

24. Ya juya waje ɗaya ya yi kuka, sai ya sāke komawa wurinsu ya yi magana da su. Ya ɗauki Saminu daga cikinsu ya ɗaure shi a kan idonsu.

'Yan'uwan Yusufu Suka Komo Kan'ana

25. Yusufu ya umarta a cika tayakan da hatsi, a kuma mayar wa kowa da kuɗinsa cikin taikinsa, a kuma ba su guzuri don hanya. Haka kuwa aka yi musu.

26. Suka labta wa jakunansu hatsi, suka tashi.

27. Da ɗaya daga cikinsu ya buɗe taikinsa domin ya ba jakinsa tauna a zango, sai ya ga kuɗinsa a bakin taikinsa.

28. Ya ce wa 'yan'uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!”Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”

29. Sa'ad da suka zo wurin mahaifinsu Yakubu a ƙasar Kan'ana, suka faɗa masa dukan abin da ya same su, suna cewa,

30. “Mutumin, shugaban ƙasar, ya yi mana magana da gautsi, ya ɗauke mu a magewayan ƙasa.

31. Amma muka ce masa, ‘Mu amintattu ne, mu ba magewaya ba ne.

32. Mu sha biyu ne 'yan'uwan juna, 'ya'ya maza na mahaifinmu, ɗayan ya rasu, autan kuwa yana tare da mahaifinmu a yanzu haka a ƙasar Kan'ana.’

33. “Sai mutumin, shugaban ƙasar, ya ce mana, ‘Ta haka zan sani ko ku amintattu ne, ku bar ɗan'uwanku ɗaya tare da ni, ku ɗauki hatsi domin iyalanku mayunwata, ku yi tafiyarku.

34. Ku kawo mini autanku, da haka zan sani ku ba magewaya ba ne, amma amintattu ne, zan kuma ba ku ɗan'uwanku, ku yi ta ciniki a ƙasar.’ ”

35. Da zazzagewar tayakansu ga ƙunshin kuɗin kowannensu a cikin taikinsa. Sa'ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshin kuɗinsu, suka razana.

36. Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.”

37. Ra'ubainu kuwa ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe 'ya'yana biyu maza idan ban komo da shi ba, ka sa shi a hannuna, zan kuwa komo maka da shi.”

38. Amma ya ce, “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.”