Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 42:28-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Ya ce wa 'yan'uwansa, “An mayar mini da kuɗina, ga shi nan a taiki!”Zuciyarsu ta karai sai suka juya suna duban juna, suna makyarkyata suna cewa, “Me ke nan da Allah ya yi mana?”

29. Sa'ad da suka zo wurin mahaifinsu Yakubu a ƙasar Kan'ana, suka faɗa masa dukan abin da ya same su, suna cewa,

30. “Mutumin, shugaban ƙasar, ya yi mana magana da gautsi, ya ɗauke mu a magewayan ƙasa.

31. Amma muka ce masa, ‘Mu amintattu ne, mu ba magewaya ba ne.

32. Mu sha biyu ne 'yan'uwan juna, 'ya'ya maza na mahaifinmu, ɗayan ya rasu, autan kuwa yana tare da mahaifinmu a yanzu haka a ƙasar Kan'ana.’

33. “Sai mutumin, shugaban ƙasar, ya ce mana, ‘Ta haka zan sani ko ku amintattu ne, ku bar ɗan'uwanku ɗaya tare da ni, ku ɗauki hatsi domin iyalanku mayunwata, ku yi tafiyarku.

34. Ku kawo mini autanku, da haka zan sani ku ba magewaya ba ne, amma amintattu ne, zan kuma ba ku ɗan'uwanku, ku yi ta ciniki a ƙasar.’ ”

35. Da zazzagewar tayakansu ga ƙunshin kuɗin kowannensu a cikin taikinsa. Sa'ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshin kuɗinsu, suka razana.

36. Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.”

37. Ra'ubainu kuwa ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe 'ya'yana biyu maza idan ban komo da shi ba, ka sa shi a hannuna, zan kuwa komo maka da shi.”

38. Amma ya ce, “Ɗana ba zai gangara tare da ku ba, ga ɗan'uwansa ya rasu, shi kaɗai kuwa ya ragu. Zai yiwu a kashe shi a hanya. Na tsufa ƙwarai ba zan iya ɗaukar wannan baƙin ciki ba, zai kashe ni.”

Karanta cikakken babi Far 42